Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Na Cigaba da Samun Galaba kan Boko Haram


Sojojin Najeriya suna sintiri
Sojojin Najeriya suna sintiri

Sojojin Najeriya sun samu sun fara bude hanyoyin jihar Borno da 'yan Boko Haram suka mamaye da nakiyoyi da bamabamai

Mai magana da yawun sojojin Najeriya Kanal Sani Kukasheka Usman yace sun bude hanyar da ta taso daga Gwozah zuwa Yamkete har wucewa Maiduguri. Dama can ‘yan kungiyar Boko Haram sun mamaye yawancin hanyoyin jihar Borno tare da shifida masu nakiyoyi da bamabamai yadda mutane basa iya yin anfani dasu sai dai wadanda suka shirya zuwa lahira.

Kanal Sani Kukasheka Usman yace sojojin dake fafatawa da ‘yan ta’adan sun kuduri aniyar cire duk nakiyoyin da ‘yan tawayen suka binne a tituna musamman a jihohi ukun nan dake arewa maso gabashin kasar. ‘Yan tawayen sun dasa bama bamai da nakiyoyi a kusan kowace hanya. Sojoji na kokarin binsu daya bayan daya suna lalatasu.

Kanal Usman yace an basu aikin kawar da duk ‘yan ta’ada tare da bude duk hanyoyin da suka dasa masu bamabamai da makamai.

Yace ‘yan tawayen sun mayar da dakin gwajin makarantar noma dake Dikuwa ya zama inda suke sarafa bamabamai.

Bayan da sojoji suka kwato garin sun samu dimbim bamabamai da nakiyoyi da kayan hadasu birjik.

Kalamun Kanal Usman sun biyo bayan wani rahoto ne dake cewa wai wakilan ‘yan Boko Haram suna neman daidaitawa da gwamnati.

Amma masu nazari da lamuran dake faruwa suna ganin nasarar da sojojin Najeriya ke samu kansu ya sa suna neman a zauna a yi sulhu.

Sai dai Kanal Usman yace sojoji ba zasu yadda ‘yan ta’adan su ja hankalinsu kan wani batun yin sulhu ba.

Kanal Usman yace ba abun mamaki ba ne idan ‘yan Boko Haram na neman a zauna a yi sulhu. Yace amma kada a manta cewa wadannan mutane ne da suka ragargaza wani bangaren Najeriya cikin shekaru shidan da suka gabata.

Kanal Usman yace saboda haka a yi takatsantsan. Kada a yadda da duk wani abun da zasu fada yanzu sai da cikakken tabbaci tare da kwakwaran matakai daga wurinsu. Amma kafin nan sojoji zasu cigaba da tarwatsasu koina aka samesu domin "muna nemansu".

XS
SM
MD
LG