Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Ce Sun Kashe 'Yan Boko Haram Da Dama


Air Marshal Sadique Abubakar

A wani cigaba a fagen yaki da 'yan ta'addan Boko Haram, runduanr sojin Najeriya ta ce ta aika da wasu 'yan kungiyar Bako Haram da dama zuwa lahira.

Hedkwatar Rundunar Sojojin saman Najeriya ta ce jiragen yakinta sun kashe mayakan Boko Haram masu yawan gaske a arewacin jihar Borno.

Kakakin rundunar, Air Commodore Ibikunle Daramola, ya ce sun sami bayannan sirri cewa mayakan Boko Haram sun yo Kaura daga yankin tafkin Chadi inda suka kafa wani sabon sansani a wajajen yankin Talala, Ajigin da Buk.

Saboda haka sai aka sake tura wasu kuramen jiragen leken asiri don kara tantancewa da kuma tabbatar da yawan mayakan, wadanda suka yi gidaje karkashin duhuwar bishiyoyin da ke yankin a Talala, nan take kuma Jiragen yakin sojojin saman Najeriyar dake karkashin rundunar Operation Lafiya Dole suka tunkari wurin Kuma suka rugurguza sansanin, aka kashe yan ta'addan masu yawan gaske.

Ga wakilinmu a Abuja Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG