Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Kai Farmaki a Wata Kasuwar Mayakan Boko Haram 


Sojojin Najeriya a Maiduguri

Wata sanarwa daga rundunar sojan Najeriya ta ce ta kai farmaki a wasu wuraren mayakan Boko Haram a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, ciki har da wata kasuwar mayakan. 

Da safiyar ranar Laraba 26 ga watan Janairun 2022, dakarun Najeriya na runduna ta musamman ta 25 da ke Damboa a jihar Borno suka lalata tare da kona wata kasuwa da aka gano ta ‘yan Boko Haram ko ISWAP ce da ke ci da dare a Gumsuri.

Rundunar sojan Najeriya ce ta sanar da hakan a wani sako da ta rubuta a shafinta na Twitter. Sai dai bata bada karin bayani ba.

Wannan na zuwa ne bayan wani hari da Sojojin runduna ta 401 tare da hadin gwiwar runduna ta 19 da ke Baga suka kai, inda suka hallaka wasu ‘yan ta’addan suka kuma wargaza daularsu ta ISWAP tsakanin Cross Kauwa da Gudumbali a jihar Bornon Najeriya ranar Talata 25 ga watan Janairu, a cewar sanarwar.

Mayakan ISWAP dai sun dade suna kai hare-haren da suka yi sanadiyyar kisan dubban mutane a yankin arewa maso gabashin Najeriya, miliyoyin wasu kuma suka kauracewa matsugunnansu. Borno na daga cikin jihohin da hare-haren ‘yan ISWAP suka shafa.

XS
SM
MD
LG