Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Kubutar Da Dubban Mutane Daga Boko Haram


Operation Lafiya Dole

Rundunar sojan Najeriya na Operation Lafiya Dole dake garin Maiduguri, tace ta samu nasarar kubutar da wasu mutane 7,896 daga hannun ‘yan kungiyar Boko Haram.

Kwamandan rundunar major janar Lucky Irabor, shine ya bayyana hakan a wata hira da yayi da manema labarai a garin Maiduguri, yace cikin mutanen akwai kuma wasu mutane ‘yan kasashen waje guda takwas, wanda kuma suka hada da maza 914 da mata 2,388 da kuma kananan yara fiye da dubu biyu.

Baki daya mutanen an samu kubutar da su ne a wurare daban-daban a sakamakon ci gaba da kakkabe sauran ‘yan kungiyar Boko Haram din da ake.

Kwamandan yace ranar 1 ga watan Fabarairun wannan shekara sun sami nasarar kashe wasu ‘yan Boko Haram guda shida, a wata arangama da suka kai musu a kauyen Dasula dake karamar hukumar Dambua. Haka kuma a ranar 7 ga watan Fabarairun kuma sun kashe wasu ‘yan Boko Haram din guda 13.

Haka kuma rundunar ta kama tabar wiwi mai yawan gaske a wajen wani mutum da ya bayyana kansa a wajen wani dake bayyana kansa a matsayin ‘dan sanda wanda ke dauke da katin shaidar zama ‘dan sanda na jabu, a yankin Son dake iyaka da jahar Borno.

Domin karin bayani saurari rahotan Haruna Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:10 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG