Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Kubutar Da ‘Yar Bautar Kasa Daga Hannun Boko Haram


Halima Umar 'yar bautar kasa da sojoji suka ceto daga Boko Haram
Halima Umar 'yar bautar kasa da sojoji suka ceto daga Boko Haram

Rundunar sojojin Najeriya shiyya ta bakwai dake garin Maiduguri, ta mika wata ‘yar bautar ‘kasa da ‘yan kungiyar Boko Haram su ka sace ga gwamnatin jihar Borno.

Tun a watan Janairun wannan shekara ne aka sace ‘yar bautar kasan mai suna Halima Umar, a kan hanyar Goza zuwa garin Maiduguri. Wanda tun wancan lokacin babu ita ba duriyarta.

Rundunar sojin ta ce ta samu nasarar ceto matar ne sakamakon aikace-aikace da suke yi a dazuka, an dai mika matar ne ga gwamnatin jihar Borno.

Kwamandan rundunar sojin dake garin Maiduguri Birgediya Janar Bulama Biu, shine ya mika Halima ga mataimakin gwamnan jihar Borno Alhaji Umar Kadafur. Wanda kuma ya mika godiya da jinjina ga jami’an tsaron game da ayyuakan da suke gudanarwa a jihar.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Haruna Dauda Biu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG