Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Shiga Dajin Sambisa


Sojojin Najeriya

Sojojin Najeriya dai na ta dada kutsa kai zuwa mafakar 'yan boko haram don ganin sun kawo karshen ta'addancin da ya addabi jama'a.

Kamar yadda rahotanni suka nuna dakarun sojojin Najeriya shine cewa sun kutsa kai cikin dajin Sambisa wanda shi kansa kakakin rundunar sojojin Manjo Janar Olukolade ya tabbatar da haka.

Sai dai kamar yadda wakilinmu Ibrahim Abdulaziz ya tabbatarwa abokin aikinmu Mahmud Lalo ba wata kwakkwarar majiyar ko sojojin sun fafata da ‘yan boko haram din ba ko a’a.

Haka kuma in ba’a manta ba dajin Sambisa ne ake zaton mafakar ‘yan boko haram din saboda daji ne mai sarkakiya sosai.

Haka kuma dakarun makwabtan Najeriya kamar su Kamaru da Chadi sun tsare kan iyakokin kasarsu koda sojojin Najeriya sun fatattaki ‘yan boko haram din sais u kuma su datse su a nan ba tare da sun kutsa cikin kasashensu ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00

XS
SM
MD
LG