Accessibility links

Sojojin Nijeriya sun kama wani kwamandan Boko Haram

  • Ibrahim Garba

Jami'an tsaro kenan ke sintiri a birnin Kano

Dakarun tsaro a Nijeriya sun ce sun kama wani babban kwamandan

Dakarun tsaro a Nijeriya sun ce sun kama wani babban kwamandan masu tsattsauran ra’ayin Islama na Boko Haram.

Wani wakilin Muryar Amurka ya ce an kama mutumin ne a yau Jumma’a a birnin Kano da ke arewacin kasar. Rahotannin kafafen yada labarai a wajejen, sun bayyana mutumin da suna Suleiman Mohammed, kuma wai an kama shi ne da matarsa da ‘ya’yansu 5, a wani samamen da aka kai gidansa.

Jami’an tsaro sun kuma sami wani akwatin makamai da kuma bama-baman da ake hadawa a gida.

Kungiyar ta Boko Haram ta kai dinbin hare-hare a sassan arewacin Nijeriya cikin shekaru 2 da su ka gabata. A watan Janairu, ta dau alhakin kai jerin hare-haren bam da mota da kuma harbe-harbe a birnin na Kano da su ka yi sanadin mutuwar mutane sama da 180.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG