WASHINGTON DC —
Babban Hafasan sojan saman Nigeria, Air Marshal Abubakar Sadeeq yace hango yadda ‘ya’yan kungiyar Boko Haram ke sake tattaruwa a dajin Sambisa ne yasa suka kai musu hari.
Yace zasu ci gaba da shawagi a wannan wurin tare da fasa su a duk lokacin da yan ta’addar suka sake yunkurin sake gamewa wuri guda.
Yanzu haka dai an kashe da dama daga cikin kwamandojojin wadannan ‘yan kungiyar.
Ga Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Facebook Forum