Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Saman Najeriya Sun Kafa Cibiyar Bincike Da Inganta Fasaha


Shugaba Muhammad Buhari a dakin cibiyar bincike da inganta fasaha ta Sojojin Saman Najeriya
Shugaba Muhammad Buhari a dakin cibiyar bincike da inganta fasaha ta Sojojin Saman Najeriya

Rundunar sojojin saman Najeriya, bayan ta kirkiro wani jirgin leken asiri da shugaban kasa ya kaddamar, ta kuma kafa cibiyar bincike da ingata fasaha wadda ta yi anfani da ita wurin gyara jiragen da basu da matuka da kuma kirkiro wasu kayan aikin.

Babban Hafsan Hafsoshin sojojin saman Najeriya Air Marshal Sadique Abubakar ya sanar da kafa cibiyar bincike da inganta fasaha da rundunarsa ta kafa a jihar Kaduna. Cibiyar data kunshi injiniyoyin sojojin sama suka hada gwiwa da bangaren kimiyya da fasaha ta rundunar, wajen samar da cibiyar.

Yace sun taka rawar gani da dama kuma za'a nuna kadan daga cikin kayan da suka kirkiro. A cewar babban Hafsan, cibiyar ta samu nasarar gyara jiragen leken asiri marar sa matuka da suka baci watannin da suka gabata saboda rashin kayan gyara. Yanzu haka jiragen suna arewa maso gabas inda suke aiki tukuru.

Air Commodore Tijjani Gamawa masanin tsaro ne da yayi aiki a rundunar sojin saman Najeriya, yace irin shugabancin da sojojin ke dashi yanzu ne ya taimaka aka samu ci gaba. Sojojin na iya yin wasu abubuwan da ba sai an fita waje an kawo ba.

A saurari rahoton Hassan Maina Kaina don karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:28 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG