Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Tunisia Suna Gadin Tashoshin Ruwan Kasar Domin...


Wani jami'in 'yansanda yake wuce gungun bakin haure daga Tunisia a Italy.

Sojojin Tunisia suna tsaron tashoshin ruwan kasar domin hana tururuwar bakin haure daga kasar zuwa Turai,abinda ya biyo bayan boren jama’ar kasar

Sojojin Tunisia suna tsaron tashoshin ruwan kasar domin hana tururuwar bakin haure daga kasar zuwa Turai,abinda ya biyo bayan boren jama’ar kasar da ya hambare gwamnatin mutuminda ya juma yana mulkin kasar.

Kusan ‘yan Tunisia dubu biyar ne suka isa wani dan karamin tsibirin Lampedusa dake kasar Italiya cikin ‘yan kwanaki da suka wuce.

Frayin ministan Italiya Silvio Berlusconi, yana kira ga tarayyar Turai ta tallafawa kasar da dala milyan 135 domin taimakawa kasar ta maganace abinda ya kira jinkai na gaggawa.

Ma’aikatar harkokin wajen Tunisia ta ki amincewa da bukatar Italiya na neman ta tura ‘yansandanta zuwa Tunisia. Ma’aikatar tace bazata kyale ko wani irin mutum yaketa diyaucinta,ko ya yi katsa landan cikin harkokin cikin gidanta ba.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG