Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sokoto: Gwamna Tambuwal Ya Angwance


Alhaji Aminu Waziri Tambuwal a lokacin wata ziyara da ya kawo Muryar Amurka ya na Kakakin Majalisa

Rahotanni daga jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa, gwamnan jihar Barrister Aminu Waziri Tambuwal ya yi amarya.

Bayanai sun nuna cewa gwamnan ya auri Maryam Mustapha wacce rahotanni suka nuna cewa sun jima suna soyayya. Maryam ta fito ne daga Jihar Kano

An dai daura auren ne a jihar ta Kano a ranar juma’ar da ta gabata, amma a cikin sirri ba tare da an yayata lamarin ba.

Wasu na kusa da gwamnan ba su musanta auren da Tambuwal ya yi ba, sai dai sun gayawa Muryar Amurka cewa batun auren lamari ne da ya shafi rayuwarsa ta sirri.

Mutane da dama a jihar sun nuna mamakinsu bayan da batun auren ya fito fili inda suka rinka mai fatan alheri.

Saurari wannan rahoto na Murtala Faruk Sayinna domin jin karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG