Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Somalia Zata Gudanar da Zaben Hadin Gambiza Badi


Shugaban Somalia Hassan Shaikh Muhammad
Shugaban Somalia Hassan Shaikh Muhammad

Shugabannin siyasa na kasar Somalia sun amince da gudanar da zabe shekara mai zuwa bisa wani tsari kamar na hadin gambiza inda za'a zabi wakilai bisa ga kabila ko addiniko bangaranci

Daga Somalia kuma, shugabannin kasar dama na yankuna sun tashi daga wani taro na kwanaki uku da sukayi a Mugadishu babban birnin kasar, kan hanyoyi da zasu fi dacewa su bi domin a gudanar da zaben kasar cikin shekara mai zuwa.

Shugabannin sun tsaida shawarar zasu rusa gwanatin kasar cikin watan Satumba mai zuwa, amma basu hana shugaban kasa- Hassan Sheikh Mohammed, da wakilan majalisar dokokin kasar, su metan da saba'in da biyar sake yin takara ba.

Hakan nan taron ya zartas da shawarar gudanar da zabe mai zuwan kan bin tsarin kabilu ko zaben gamin gambisa da shugabannin kabilu ko dangi zasu fitar da wakilai daga cikinsu.

Gwamnatin kasar ta farko bayan yakin basasar da kasar ta shiga na lokaci mai tsawo, shugabannin kabilu ne suka zabe su bayan da suka hadu a Mugadishu a shekarar ta 2012.

XS
SM
MD
LG