Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Somaliland Ta Kammala Zaben Shugaban Kasa


Muse Bihi Abdi dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar dake mulki

Somaliland, kasar da ta balle daga Somalia saboda rikicin kasar da al-Shabab ta haddasa ta kammala gudanar da zaben shugaban kasa yanzu kuma ana kidaya kuri'un da aka kada

Ana kidaya kuri’u a Somaliland bayan da jamhuriyar da ta balle ta gudanar da zaben shugaban kasa.

‘Yan takara uku ne suka yi takarar maye gurbin shugaban kasa Ahmed Mohammed Mohamoud, wanda yaki sake tsayawa takara.

Mata suna kada kuri'a akasar Somaliland
Mata suna kada kuri'a akasar Somaliland

Hukumar zaben Somaliland tace an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali a yankuna shida na jamhuriyar. Tace an sami faruwar wani tashin hankali ‘daya tal a yankin Togher, inda a kalla mutum guda ya ji rauni bayan da wani soja ya harba bindigar sa bisa kuskure.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG