Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Somaliya Ta Haramta TikTok, Telegram Da 1XBet Don Dakile Yaduwar Batsa


Wasu Matasa ‘Yan Kasar Somaliya
Wasu Matasa ‘Yan Kasar Somaliya

Somaliya ta bi sahun wasu kasashe wajen haramta TikTok, da kuma hanyar aika sakon Telegram da gidan yanar gizo na 1XBet domin dakile yada ayyukan batsa da lalata da wasu abubuwan da ba su dace ba da kuma farfaganda, in ji ministan sadarwar kasar

WASHINGTON, D.C. - “Ministan sadarwa ya umarci kamfanonin intanet da su dakatar da aikace-aikacen da aka ambata a baya, wadanda ‘yan ta’adda da kungiyoyin fasikanci ke amfani da su wajen yada munanan hotuna da kuma labaran karya ga jama’a,” in ji Ministan, Jama Hassan Khalif a wata sanarwa da ya fitar a yammacin Lahadi.

Mambobin kungiyar masu ta da kayar baya ta Al-Shabaab sukan yada ayyukansu ne akan TikTok da Telegram.

Matakin na zuwa ne kwanaki bayan shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamud, ya ce, farmakin soji kan kungiyar Al-Shabaab na da nufin kawar da kungiyar da ke da alaka da Al-Qaeda nan da watanni biyar masu zuwa.

TikTok, Telegram da 1XBet nan take ba su ce uffan ba, a lokacin da Reuters ya nemi su yi tsokaci kan lamarin.

Umurnin ya ba masu ba da sabis na intanet su fara aiwatar da wannan tsari nan da zuwa ranar 24 ga watan Agusta.

An yi barazanar haramta TikTok da saka masa takunkumi a Amurka saboda alakarta da Gwamnatin China.

Jihar Montana ta zama ta farko da ta haramta amfani da manhajar a watan Mayu.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG