Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Somaliya Ta Kori Speto Janar Na 'Yansanda Da Shugaban Hukumar Leken Asiri.


Baraguzan motar da aka kai hari da ita a Mogadishu ranar Asabar.
Baraguzan motar da aka kai hari da ita a Mogadishu ranar Asabar.

Hakan ya biyo bayan harin da aka kai ranar Asabar har mutane akalla 26 suka halaka.

A somaliya gwamnatin kasar ta kori babban baturen 'Yansanda da babban jami'in hukumar leken asirin kasar, bayan wani mummunar hari da kawanyar da mayakan al-shabab suka yi wa wani O'tel a Mogadishu babban birnin kasar.

Jami'ai suka ce an kashe akalla mutane 26 a harin da aka kai kan O'tel din da ake kira Nasa Hablod Two. Wasu mutane mnasu yawa kuma sun jikkata a fashewar.
Mayakan sakan sun kutsa cikin O'tel din jiya Asabar, bayan da suka tada nakiyoyi da suka dankarawa wata mota a kofar shiga O'tel din.

'Yansanda suka ce sun kama biyu daga cikin maharan suka kashe biyu daga cikin su.

Kungiyar al-shabab ta dauki alhakin kai wannan hari.

Sakamakon haka ne baturen 'Yansandan kasar Janar Abdihakhim Dahir Saaid, da shugaban hukumar leken asirin kasar Abdullahi Mohammed Ali Sanbalolshe suka rasa ayyukansu, kamar yadda ministan yada labarai Abdirahman Omar Osman ya sanar ta shafinsa na Tweeter.

Akwai bam na biyu da ya tashi a jiyan kusa da tsohon ginin majalisar dokokin kasar. Babu cikakken bayani irin barnar da fashewar ta haddasa a wurin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG