Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Somaliya Za Ta Kaddamar Da Wani Gagarumin Yaki Kan Al-Shabab


Dubban 'yan Somaliya sun taru don addu'o'i da makoki
Dubban 'yan Somaliya sun taru don addu'o'i da makoki

Ga dukkan alamu za a shiga dauki ba dadi tsakanin sojojin Somaliya da kungiyar al-Shabab, sanadiyyar mummunan harin nan na ranar Asabar da ta gabata, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama. Tuni Shugaban kasar ya sha alwashin mai da martani mai tsanani.

Dubban 'yan Somaliya sun taru jiya Jumma'a a wurin da aka kai harin nan mafi muni a tarihin kasar ranar Asabar din da ta gabata, lokacin da wata motar daukar kaya ta tarwatse a wata cinkusasshiyar hanya a birnin Mogadishu, inda mutanen da su ka mutu zuwa yanzu ya kai wajen 358.

Yayin da 'yan Somaliyan su ta taru a babban birnin kasar ta su don yin makokin, Faraministan Somaliya ya ce Shugaban kasar zai yi shelar kaddamar da yaki kan kungiyar al-Shabab, tsattsaurar kungiyar da gwamnatin kasar ke zargi da kai harin na bom.

Shugaban kasar Mohammed Abdullah Mohammed Imam, ya gaya ma kafar labarai ta Associated Press cewa sabon farmakin da za a kai, zai kunshi dubban sojojin kasar, wadanda za su yi kokarin fatattakar al-Shabab daga tungayensu na Shabelle Ta kasa da kuma yankin Shabelle ta Tsakiya; inda aka yi imanin cewa daga nan ‘yan kungiyar ta al-Shabab su ka shirya harin da su ka kai Mogadishun.

Jiya Jumma'ar ma rundunar sojin Amurka, ta ce ta kaddamar da wani hari kan al-Shabab da jirgi mara matuki, ta koma yaki da kungiyar 'yan bindigar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG