Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Spain Ta Hana A Gudanar Da Zaben Raba Gardaman 'Yancin Kai A Catalonia


Magoya bayan kuri'ar raba gardama 'yancin kai a Catalonia a Spain

Yau ne Catalonia ta shirya zaben raba gardama kan neman 'yancin kan yankin daga Andalusiya.

Spain ko Andalusiya, tana son ta hana zaben raba gardama na neman 'yan cinkai da yankin kasar da ake kira Catalonia suka shirya. Ta kira "zaben shirme."

Enric Millo, wakilin Madrid a yankin Catalonia, yace shugaban yankin Carles Puigdemont, da tawagarsa ne "hakkin dukkan abunda ya faru yau, da kuma duk abunda zai faruidan basu kawo karshen wannan shirmen ba."

'Yansanda cikin damara sun yi amfani da guduma suka fasa kofar shiga wata tashar zabe inda ake s a ran ashugaban yankin na Catalonia zai kada kuri'ar raba gardamar a yau Lahadi, a zaben da hukumomin Andalusiyan ko Spain suka haramta.

Arangama ta barke tsakanin 'Yansanda masu zabe a harabar wata cibiyar zabe a Sant Julia de Ramis, dake kusa da birnin Girona.
Shugaban yankin Carles wanda ada aka shirya zai kada kuri'arsa a Sant Julia de Ramis, ya jefa kuri'arsa ce a wuri da ake kira Cornella del Terri a lardin da ake kira Girona.

Mazauan yankin na Catalonia sun fara kada kuri'unsu ne a zaben raba gardamar da ake rikici akai, yayinda 'Yansanda suka kwace katunan zabe a akalla wata tashar zabe daya.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan Spain ta fada a shafin Twittter cewa,'Yansanda zasu kwace karin akwatunan zabe a ci gaba da tura su zuwa yankin.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG