PM Spain, PM kasar Mariono Rajoy, ya bada sanarwar yau Asabar cewa zai kori gwamnatin yankin Catalonia mai shirin ballewa, sannan a yi sabon zabe, a wani yunkuri na hana yankin mai kwariya-kwariyar cin gashin kai daga ayyana 'yancin gashin kai.
PM Rajoy, ya bada wanan sanarwar ce bayan da majalisar ministocin kasar da yake yiwa jagoranci tayi wani zaman gaggawa yau Asabar domin tunkarar rikicin siyasar data kunno kai sakamakon yunkurin ballewar da shugabannin yankin na Catalonia suka ayyana.
A ranar Alhamis gwamnatin ta Spain ta fara daukar matakai na janye kwariya-kwariyar 'yancin da yankin na Catalonia yake dashi.
Facebook Forum