Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Su Wane Ne 'Yan Wasan Kwallon Golf Mafiya Dukiya a Duniya?


 Tiger Woods na Amurka
Tiger Woods na Amurka

Assalamun Alaikum, dafatan Mai Saurare na cikin koshin Lafiya; barkanmu da sake saduwa a wani sabon shirin Takaitattun Labaran Wasanni dake zuwa akwatunan radiyoyinku a dai-dai wannan lokaci, wanda ni Abdulwahab Muhammad, daga Birnin Bauchin Yakubu ke shiryawa da gabatarwa, Gidan Radiyon Muryar Amurka ke Cillo muku daga Birnin Washington DC, na Amurka.

Zan fara ne da kawo muku jerin sunayen 'Yan wasan Golf Mafiya Arziki a Duniya su guda goma, wanda aka bayyana a shekarar nan damu ciki ta 2022.

Mutum na farko shi ne, Tiger Woods, ya na da dalar Amurka, miliyan dari takwas, ($800) sai mabi masa, wato mutum na biyu, Arnold Palmer, yana da zunzurutun dalar Amurka, diliyan Dari bakwai, ($700), sai na uku, Greg Norman, yana da dalar Amurka, miliyan dari biyar, ($500), mutum na hudu, Phil Mickelson yana da dalar Amurka, miliyan, dari hudu, $400 Million.

Arnold Palmer
Arnold Palmer
Greg Norman
Greg Norman

Mutum na biyar shi ne, Jack Nicklaus, yana da dalar Amurka miliyan dari uku da ashirin $320, mutum na shida a yawan masu kudin duniya 'yan wasan Golf, shi ne , Gary Player, yana da kudi dalar Amurka , miliyan dari biyu da hamsin da biyar, $255 million, mutum na bakwai, shine, Rory McCilroy, yana da dalar Amurka miliyan dari biyu da ashirin, $220, Fred Couples,shne mutum na takwas a jerin sunayen yan wasan Golf, masu kudi a duniya shi yana da dalar Amurka miliyan dari da ashirin da biyar

Saurari cikakken rahoton Abdulwahab Muhammad:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:03 0:00

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG