Accessibility links

Sudan Da Sudan Ta Kudu Sun Koma Teburin Shawarwari

  • Aliyu Imam

Shugaban Sudan ta kudu Salva Kiir (C) da takwaran aikinsa na Sudan al-Bashir, cikin farin kaya.

An bada rahoton cewa Sudan ta janye sojojinta daga yankin Abyei mai arzikin mai da suke gardama akai.

An bada rahoton cewa Sudan ta janye sojojinta daga yankin Abyei mai arzikin mai da suke gardama akai, jim kadan bayan kasashen biyu makwabta suka koma kan teburin shawarwari yau talata.

Cibiyar labarai wacce take da alaka da gwanatin kasar ta Sudan , tace sojojin Sudan sun mika kayan aiki a yankin Abyei ga hanun sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD. Sudan ta kudu ta janye sojojinta daga yankin a farkon watan nan.

Ahalin da ake ciki kuma mashawarta daga kasashen biyu sun kaddamar da shawarwari kai tsaye a karo farko tun cikin watan Maris lokacin da fada ya barke kan iyakokin kasashen biyu.

Tarayyar Afirka ce take shiga tsakani a shawarwarin da ake yi a Addis Ababa. Sudan da Sudan ta kudu suna gardama sakamakon ballewar Sudan ta kudu a bara, galibi kan batun shata iyaka, da kuma rabon arzikin mai.

A wani lamari na daban kuma, shugaban Somalia Sheikh Sharif Sheikh Ahmed ya tsallaka rijaya da baya, bayan wani yunkurin halaka shi da kungiyar al-shabab taso yi.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG