Accessibility links

Sudan ta Kudu da Sudan ta arewa sun gwabza a kan iyakar da su ke takaddama akai

  • Ibrahim Garba

Wasu dakarun Sudan

Sudan ta kudu ta zargi Sudan (ta arewa) da kaddamar da harin jirgin sama

Sudan ta kudu ta zargi Sudan (ta arewa) da kaddamar da harin jirgin sama a kanta a rana ta biyu a yankin da ke da arzikin man fetur, da ke kan iyakar da su ke takaddama akai, kwana guda bayan wata fafatawar soji kai tsaye da ba a saba gani ba tsakanin abokan gaban biyu.

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya ce mayakan saman Sudan (ta arewa) sun jefa bama-bamai kan wasu wurare biyu a jihar Unity. Y ace bayan harin bama-baman sai kuma dakarun Sudan (ta arewa) su ka kai hari kan Sudan ta Kudu, to amman wai sun fatattake su.

Tunda farko Ministan Sadarwar Sudan ta Kudu, Barnaba Benjamin y ace Shugaban kasar y ace Sudan ta Kudu ba za ta shiga yaki mara kan gado da Sudan (ta arewa ba).

Wasu jami’an Ma’aikatar Harkokin Wajen Sudan (ta Arewa) sun ce matakan da dakarun Sudan (ta arewa) su ka dauka martani ne na wani mummunan harin da dakarun Sudan ta Kudu su ka kai masu.

Tashin hankalin ya auku ne kwana guda bayan da bangarorin biyu su ka zargi dakarun juna da ketara kan iyakar juna, wadda wata iyaka ce da ba a shata ta da kyau ba da ta raba kasashen biyu. Dukkannin bangarorin biyu sun yi ikirarrin cewa sun dau matakin kare kansu ne kuma sun yi shelar samun nasara bayan fadan. Ba a dai tantance adadin wadanda abin ya rutsa da su ba.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG