Accessibility links

Sudan ta Kudu ta ba da shawarar a ware gandun dajin da ba soja ciki

  • Ibrahim Garba

Wakilan Sudan da Sudan ta Kudu a Wurin tattaunawar

Kudancin Sudan ta bayar da shawarar a ware wani babban yankin da za a hana soja shiga

Kudancin Sudan ta bayar da shawarar a ware wani babban yankin da za a hana soja shiga a kusa da kan iyakarta da abokiyar gabanta Sudan – shawarar da Sudan ta yi maza ta ki.

Wannan shawarar ta zo ne a jiya Laraba a wurin tattaunawar da kungiyar tarayyar Afirka ke daukar nauyinta da zummar sasanta takaddamarsu da kuma rage tayar da jijiyoyin wuya tsakanin makwabtan da su ka sha fafatawa da juna a kan iyakarsu.

Ministan Kudancin Sudan Nhial Deng ya ce shawarar ta tanaji cewa dukkannin bangarorin biyu su janye dakarunsu da nisan kilomita 10 daga kan iyaka.

To amman kakakin wakilan Sudan Omer Dahab ya yi watsi da shawarar. Da ya ke magana da ‘yan jarida, ya ce gandun daji irin wannan zai kunshi Heglig mai arzikin man fetur, wanda Sudan ta kwato bayan da dakarun Sudan ta Kudu su ka mamaye wurin a cikin watan Afrilu.

Jerin tattaunawa a Addis Ababa babban birnin Kasar Habasha bai kawo wani cigaba na azo a gani ba.

Sudan da Sudan ta Kudu na jayayya kan iyaka da man fetur da kuma batun dan kasa wadanda su ka biyo bayan samun ‘yancin kan Kudu a watan yulin bara. Tashe-tashen hankula na baya-bayan nan game da kan iyaka sun tayar da fargabar yiwuwar kasashen sun fada yaki gadan-gadan.

XS
SM
MD
LG