Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SUDAN TA KUDU: Tana Neman Karin Makwanni Biyu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya


Taron kulla yarjejeniya akan wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu a karkashin shugabancin Majalisar Dinkin Duniya

Kasar Sudan ta Kudu tace tana bukatar karin makwanni biyu domin yin nazari game da batun cimma yarjejeniya da yan tawayen kasar abinda yasa shugaba Salva Kirr yaki sa hannu ga takaddar yarejeniyar kenan.

Ministan yada labarai na kasan Micheal Ma-koi ya fada jiya Talata cewa gwamnati ba zata rattaba hannu bag a wannan yarjejeniyar sai ta tattauna da mutanen kasa tukunna domin jin menene raayin su game dawannan batu.

Shima ministan harkokin waje Barnabas Marial Benjamin yace yau ne gwamnati zata fara tattaunawa da kungiyoyi masu zaman kansu, jamiyyun siyasada kuma masu ruwa da tsaki a harkokin kasa domin tattauna yadda za a samu hanya ta sadidan kan wannan batu na samar da zaman lafiya.

Yace shugaba Saiva Kir yaki sa hannu ne domin ko masu shiga tsakani basu daidaita bayanan dake cikin kundin yarjejeniyar ba.

Sai dai a wuri daya shugaban yan tawayen Riek Machar yasa hannu a wannan yarjejeniyar a can kasar Adis Ababa tun ranar littini awoyi kafin kawo karshen waadin da kungiyar kasashen gabashin Africa suka shata.

Wannan yarjejeniyar dai shine ake sa ran ya kawo karshen yakin basasan da aka kwashe watanni 20 ana yi wanda yasa mutane sama da miliyan 2 rasa matsugunnin su.

Sai dai shugaba Kirr ya kasance cikin babban matsin lamba a jiya domin yasa hannu.

Kasar Amurka tace taji kuyya kwarai da gaske domin kasar ta Sudan ta kudu tayi watsi da damar da ta samu na ganin ta samar wa kanta zaman lafiya da mutanen ta.

Wannan kalami na kunshe a cikin bayanan da mai shugaban Amurka shawara a harkokin tsaro Susan Rice tace, kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zaiyi gaban kansa muddin gwamnatin taki sa hannu a cikin kwanaki 15 na ganin an kawo karshen wannan tashin tashina tsakanin kasar da yan tawaye

XS
SM
MD
LG