Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sudan ta Kudu: Wakilan 'Yan Twaye da Na Gwamnati Sun Yi Taron Farko


Wakilin 'yan tawaye Hassan Lako yake dariya da waikilin gwamnati gabanin soma taronsu
Wakilin 'yan tawaye Hassan Lako yake dariya da waikilin gwamnati gabanin soma taronsu

Wakilai daga bangaren ‘yan tawaye da gwamnatin Sudan ta Kudu, sun yi zama na farko, a wani yunkurin na shawo kan yakin basasan da ya addabi kasar.

Bangarorin biyu sun yi zaman ne a Juba, babban birnin kasar ta Sudan ta Kudu a jiya Talata, da fatan za a kafa gwamnatin wucin gadi, wadda za ta kunshi dukkanin bangarorin da ke takaddama.

A baya ‘yan tawayen da gwamnatin sun sha gudanar da zama, tun bayan da yakin basasan ya barke a tsakiyar watan Disamban shekarar 2013, sai dai an yi ta saba yarjeniyar tsagaita wuta da aka samar a shekarun biyun da suka gabata.

Shugaban Salva Kiir da shuagban ‘yan adawa Riek Machar, sun sha zargin juna da saba yarjeniyar zaman lafiya, amma dukkaninsu suna ikrarin cewa za su ci gaba da mutunta yerjeniyar 26 ga watan Agusta da aka kulla, duk da cewa ana saba wa’adin da aka cimma.

Sudan ta Kudu, ita ‘yar autar kasashen da suka samu ‘yan cin kai a duniya, bayan da ta balle daga Sudan a shekarar 2011.

Dubun dubatar al’umar kasar wannan rikici dai ya halaka, kana ya raba mutane miliyon biyu da muhallansu.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG