Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamhuriyar Sudan ta Kudu tayi bukin samun 'yancin kai


Wani dan Jamhuriyar Sudan ta Kudu yana rike da tutar kasar
Wani dan Jamhuriyar Sudan ta Kudu yana rike da tutar kasar

Jamhuriyar Sudan ta Kudu wadda ta gudanar a bukin ‘yancin kanta a Juba babban birnin kasar yau asabar ta kasance sabuwar kasa a duniya.

Sudan ta Kudu wadda ta gudanar a bukin ‘yancin kanta a Juba babban birnin kasar yau asabar ta kasance sabuwar kasa a duniya. Duban mutane da suka halara a wajen bukin sun yi ta ihu da guda lokacin da sojoji suka daga sabuwar tutar kasar yayinda suka kuma sauke tutar arewacin kasar. Wadanda suka halarci taron sun kuma saurari karanta ayyana ‘yancin kasar da sakonnin fatar alheri daga manyan baki dabam dabam da suka hada da shugaban arewacin Sudan Omar al-Bashir. Jamhuriyar Sudan ta Kudu ta zama sabuwar kasa a duniya a daidai karfe goma sha biyu na dare agogon kasar. Mazauna Juba sun shiga buki kan tituna, aka kuma ci gaba da bukukuwan a babban filin wasan Juba da aka sawa sunan John Garang wanda ya jagoranci dakarun kudancin Sudan a yakin basasan da aka shafe shekaru ana yi. Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir wanda yayi jawabi na karshe, ya godewa kasashe da kungiyoyin agaji da suka taimaka wajen ciyar da al’ummar kasar Sudan da kuma ilimantar da su yayinda ake rikici. Yace tilas ne mutanen kasar Sudan su yafe amma ba zasu taba mantawa da wahalar da suka sha ba. Da yake kira domin zaman lafiya, yace tilas ne kabilun dake kasarshi su fara daukar kansu da farko a matsayin ‘yan kasar Sudan ta Kudu. Ya kuma sanar da yin ahuwa ga mayakan da suka yaki gwamnatin kasar Sudan cikin watannin nan. Kudancin Sudan ta nuna gagarumin goyon bayan ballewa daga arewaci a kuri’ar raba gardamar da aka kada a watan Janairu. Wannan ya biyo yarjejeniyar warzar da zaman lafiya da aka cimma a shekara ta dubu biyu da biyar da ta kawo karshen yakin basasa da aka shafe shekaru ana yi a Sudan.

XS
SM
MD
LG