WASHINGTON D.C. —
A yau Asabar, Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir, ya ce zai mayar da kasar mai tsarin jihohi goma.
Wannan mataki na da muhimmanci kuma bukata ce da bangaren ‘yan adawa ya gabatar, domin kafa gwamnatin hadaka, a yunkurin da ake yi na kawo karshen yakin basasar kasar.
Kiir ya ce, yanzu za a raba kasar zuwa jihohi goma hade da wasu yankunan gudanar da mulki uku, wadanda suka hada da Pibor, Ruweng da kuma Abyei.
Shugaba Kiir, ya kuma yi kira ga bangaren na adawa, da shi ma ya yi sakayya ta alheri, kan wannan mataki da gwamnatin ta dauka.
Shi batun adadin jihohi a kasar, ya zama muhimmin batu a kokarin da ake yi na sasanta rikicin kasar ta Sudan ta Kudu, lura da cewa shi ne zai nuna iya iko kan yankunan da kowane bangare ke da shi.