Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sultan Ya Nemi Gwamnati Ta Sauya Manufa Kan Harajin Tsoffin Motoci


Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar III

Yau Mukaddashin Shugaban Najeriya Farfasa Osinbajo ya kai ziyarar kwana daya zuwa Sokoto inda Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya bayyana rashin jin dadinsa da wata manufar hukumar kwastan na tilastawa masu tsoffin motoci su sake biyan haraji kan motoci.

Sarkin Musulmi ya ce wannan lamarin ka iya karawa jama'a, musamman talakawa kuncin rayuwa ya kara dagula irin halin da 'yan Najeriya ke ciki.

Ya kira gwamnatin tarayya ta sake nazari akan wannan sabon shirin karbar haraji akan motoci har ma tsoffin da aka dade ana hawansu

"Wajibi ne a tabbata cewa ba'a dauki wani matakin da zai kara tsananta wa jama'a kuncin rayuwa ba" In ji Mai Martaba Sarkin Musulmi.

Sarkin ya sake tunatar da gwamnantin tarayya kan kiran da ya yi can baya akan hana shigo da shinkafa ta iyakokin kasa lamarin da ya ce ya kara ta'azzara matsalar tattalin arziki da tsadar kayan abinci

Mukaddashin shugaban kasa Farfasa Yemi Osinbajo ya kai ziyarar wuni daya ne a jihar Sokoto domin kaddamar da taron kanana da matsakaitan masana'antu ta hanyar sadasu da hukumomin gwamnati dake da alhakin ba da izinin kafa masana'antun.

Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:26 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG