Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Suluhu Ta Zama Mace Ta Farko Da Za Ta Shugabanci Tanzania


Samia Suluhu Hassan
Samia Suluhu Hassan

Masana a sha’anin mulki sun ce, Mataimakiyar marigayi tsohon Shugaban kasar Tanzaniya, John Pombe Magufuli, da ya mutu jiya Laraba, Samia Suluhu Hassan, ta kasance mace ta farko da ta dare kan kujerar shugaban kasar, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya gindaya.

A karkashin kundin tsarin mulkin kasar, Mataimakiyar marigayi Shugaba Magufuli, mai shekaru 61 a duniya, Samia Hassan, za ta karasa sauran wa’adin mulkin shugaban karo na biyu na tsawon shekaru 5, wanda zai kare a shekarar 2025.

Tsohuwar hadima a ofis kuma mai rajin cigaba, Hassan, ta fara gwagwarmayar siyasa ne a shekarar 2000 a garin ta na asali wato Zanzibar, wani yanki mai cin gashin kansa, kafin a ka zabe ta ta wakiliya a babban yankin Tanzaniya a majalisa kuma daga bisani aka ba ta mukami a babban ma’aikatar kasar.

Samia Suluhu Hassan
Samia Suluhu Hassan

Fitacciya a jam’iyyar da ke mulki, Hassan ta dare mataki zuwa mataki har lokacin da marigayi shugaba Magufuli, ya zabe ta a matsayin Mataimakiya a yayin gangamin yakin neman zabensa na farko a shekarar 2015.

Karin bayani akan: Samia Suluhu Hassan, John Magufuli, da Tanzania.

Jam’iyyar The Chama Cha Mapinduzi (CCM) ta ci zaben kuma daga nan Malama Hassan ta kafa tarihi a lokacin ta ita da marigayi Magufuli suka karbi rantsuwar kama aiki a matsayinta na mace ta farko Mataimakiyar shugaban kasa a Tanzaniya.

An sake zaben Hassan da Magufuli karo na biyu a watan Oktoba, zabe mai cike da korafe-korafen tafka magudi, kamar ‘yadda jam’iyyun adawa a kasar su ka yi zargi.

A wasu lokuta , malama Hassan na wakiltar marigayi Magufuli, a tafiye-tafiye zuwa kasashen waje, saidai yawancin mutane ba su san da ita ba ya zuwa lokacin da ta bayyana a gidan talabijin na kasar Tanzaniya sanye da bakin gyale tana bayyana mutuwar shugaba Magufuli, wanda ya rasu ya na da shekaru 61 sakamakon wata gajeriyar jinya.

Samia Suluhu Hassan Mukaddashin Shugaban kasar Tanzaiya bayan rasuwar Shugaba Magufuli.
Samia Suluhu Hassan Mukaddashin Shugaban kasar Tanzaiya bayan rasuwar Shugaba Magufuli.

A jawabinta cikin natsuwa, Malama Hassan, ta ayyana kwanani 14 a matsayin na zaman makokin rasa marigayi tsohon Shugaban kasar Tanzaniya, John Pombe Magufuli.

Samia Suluhu Hassan dai za ta yi shawara da jam’iyyar CCM game da zabar sabon Mataimakinta.

Samia Suluhu Hassan
Samia Suluhu Hassan

Masu sharhi kan lamurran siyasa a kasar dai sun bayyana cewa, Samia Suluhu Hassan, za ta fuskanci matsin lamba daga jiga-jigan siyasar kasar da ma manyan aminan marigayi Magufuli, wadanda su ka mamaye bangaren bayanan sirri da ma sauran muhimman bangarorin gwamnati, kuma za su yi kokarin yin katsalanda a ajandodinta.

Samia Suluhu Hassan, uwa ga ‘ya’ya hudu, ta yi karatu daga matakin firamare zuwa jami’a a kasashen Tanzaniya, Burtaniya da Amurka, kuma ta yi jawabin karfafa gwiwa ga mata da ‘yan mata na kasar Tanzaniya da su yi duk mai yiyuwa wajen cimma burinsu na rayuwa.

XS
SM
MD
LG