Accessibility links

Muna iya zaman awowi talatin da shida domin hakkin kuri’un mu.

A jihar Zamfara dubun dubatan jama’a, ne suka kayi zamar durshan suna jiran isowar dan takarar shugaban kasa, na jam’iyyar adawa ta APC janar Muhammadu Buhari, inda jiran nasu yazo karshe misalign karfe goma na dare, a lokacin da dan takarar ya isa garin Gusau.

A jihar Kebbi, kuma baya da dubban jama’a, da suka hallara, a dandalin wasani na Haliru Abdu, dake birnin Kebbi, wasu daruruwane suka yi tattaki da kafa na tsawon kilomita fiye talatin da biyar, daga garin Jega zuwa birnin Kebbi, domin jaddada kaunarsu ga janar Buhari.

Daya daga cikin wadanda suka yi wannan tattaki daga Jega zuwa birnin Kebbi, Sanusi Daudu Jega, yace “Ba mota ne bamu da ba ko kuma kudi shiga mot aba mun yi wannan ne don mu nunawa Najeriya, da Duniya cewa muna iya yin dukkan abunda ya wajaba gad an siyasa gad an takara domin mun tako daga Jega zuwa birnin Kebbi kilomita talatin da shida, shine muke so mu nunawa Duniya muna iya zaman awowi talatin da shida domin hakkin kuri’un mu.”

XS
SM
MD
LG