Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Rasha Na Kokarin Tantance Ko Shugaban Wagner Na Cikin Jirgin Saman Da Ya Yi Hatsari


Tsohon Hoto: Shugaban Wagner Prigozhin
Tsohon Hoto: Shugaban Wagner Prigozhin

Ana fargaban shugaban sojojin haya na Wagner Yevgeny Prigozhin ya mutu a wani hatsarin jirgin sama da ya faru a Rasha a ranar Laraba.

Jirgin ya taso ne daga birnin Moscow zuwa St. Petersburg a lokacin da ya yi hatsari, a cewar jami’an hukumar ba da agajin gaggawa ta Rasha.

Jami’an sun kara da cewa a cikin jerin sunayen fasinjojin jirgin, har da shugaban kungiyar sojin haya ta Wagner, Yevgeny Prigozhin.

Sai dai jami'an sun ce ba a tabbatar ko yana cikin jirgin ba.

Wasu rahotanni da ba a kammala tantancewa ba, sun ce jirgin mallakin Prigozhin ne, wanda shi ya kafa rukunin sojojin hayar na Wagner.

Ita ma hukumar da ke kula da sufurin jiragen sama a Rashar ta Rosaviastsia, ta tabbatar da cewa, lallai akwai sunan Prigozhin a takardar da ke dauke da sunayen fasinjan, amma babu tabbacin ko yana ciki.

Kamfanin dillancin labarai na Rasha Tass, ya ruwaito wasu jami’an ba da agajin gaggawa na cewa jirgin na dauke ne da matuka uku da wasu fasinja bakwai.

A halin da ake ciki, an kaddamar da bincike kan faduwar jirgin, wanda ya rikito kasa a yankin Tver mai nesan kilomita sama da 100 da Moscow, babban birnin Rasha.

Sojojin haya na Wagner sun marawa na Rasha baya a yakin da kasar ke yi da Ukraine.

A watan Yunin da ya gabata Prigozhin ya yi wa shugabannin dakarun Rasha bore.

Hukumomin Kremlin sun ce za a tura shi gudun hijira zuwa Belarus, yayin da aka ba dakarunsa zabin ko su bi shi, ko su yi ritaya ko kuma su shiga asalin rundunar sojin Rashar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG