Amurka ta yi na’ama da shirin tsagaita wutar da aka cimma a Lardin Idlib na kasar Syria, Lardin da ya kasance tunga ta karshe da masu ta-da kayar baya ke rike da shi, wanda ke arewa maso yammcin kasar.
Sai dai a wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar harkokin wajen Amurkan ta ce, ya zama dole a dakatar da “kai hare-hare akan fararen hula da wuraren da suke zaune.”
Mazauna yankin na Idlib, sun nuna farin cikinsu da wannan shiri na tsagaita wuta.
“Wannan shiri na tsagaita wuta yana da fuskoki biyu, na farko, mutane za su samu damar komawa gidajensu ba tare da fargabar za a kai musu hari ba, a daya bangaren kuma, shi ne ba mu san mai za a kukkulla ba a wannan lokaci na tsagaita wuta.” In ji Hassan Abdelal, wanda ke zaune a yankin na Idlib.
Kasashen Turkiyya da Rasha ne suka hada kai aka cimma wannan matsaya ta tsagaita wuta, abin da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yaba.
A daren ranar Alhamis ake fatan shirin tsagaita wutar zai fara aiki.