Yayin da cutar nan ta Coronavirus ke ta yaduwa a fadin duniya, shuwagabannin Kurdawa da kuma kungiyoyin kare hakkin dan adam, sun shiga gargadin cewa, muddin dubban mayakan ISIS da ake rike da su a arewa maso gabashin Syria suka kamu da wannan muguwar cutar, to za a ga wani babban bala’i.
Kungiyar SDF, wadda gamayya ce ta kungiyoyin sojin da Kurdawa ke jagoranta, wadda kuma ta kasance babbar kawar Amurka a yaki da kungiyar ISIS a Syria, ta ce akwai matukar yiwuwar faruwar hakan.
Sun ce sun fadi hakan ne saboda hukumomin yankin ba su da sukuni da kuma kayan aikin dakile yaduwar cutar.
“Matsawar wannan cutar ta isa wadannan gidajen yarin, za ta fi karfinmu,” a cewar Nuri Mahmud, wani babban jami’in kungiyar dakarun SDF.
Ya kara da cewa, “idan duniya ma da kanta fama ta ke yi da yaduwar wannan cutar, to kai kanka kasan da matukar wuya mu iya shawo kanta, ganin yadda muke da ragaggen karfi."
Facebook Forum