Accessibility links

Syria Ta Kusa Zama Somaliya Ko Afghsnistan?


Hoto da ke nuna hayaki yana tashi daga kan wani gini a Homs na Syria.

: Kafofin labarun masu rajin neman chanji a Syria, sun yayata labarin cewa masu tada kayar baya a Syria, sun kashe sojin Gwamnati akalla ashirin a wata fafatwar da aka yi daren jiya Talata.

Masu tada kayar baya a kasar Syria sun kashe sojin Gwamnati akalla 20.

Kafofin labarun masu rajin neman chanji a Syria, sun yayata labarin cewa masu tada kayar baya a Syria, sun kashe sojin Gwamnati akalla ashirin a wata fafatwar da aka yi daren jiya Talata. Gefe guda kuma, jagoran jami’an kallon Majalisar Dinkin Duniya yace jami’an kallon zasu ci gaba da zama a Syria domin ci gaba da aikinsu.

Jagoran jami’an kallon Majalisar Dinkin Duniya a Syria, Manjo-Janar Robert Mood yayi kukan ganin yadda al’ummar kasar Syria ke ci gaba da zama cikin ukuba da fargaba, domin al’amura sai kara kazancewa suke yi, don haka ya zama wajibi ga jami’an kallon na MDD su ci gaba da zama a Syria.

A rahoton halin da ake ciki da ya mikawa kwamatin sulhu da tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, manjo-janar Mood yace duk da kokarin kaiwa jami’an kallo harin kwanton baunar da tun farko aka nemi a janyesu, halin da ake ciki yanzu a Syria, ya tilastawa jami’an kallon ci gaba da zama. Akwai jami’an kallon Majalisar Dinkin Duniya dari uku yanzu haka a Syria, kuma basu dauke da makami.

XS
SM
MD
LG