WASHINGTON, D.C —
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce wadanda suka yi zanga-zanga ta hanyar tashin hankali a kasar, sun aikata abin da ya kira, “ta’addanci a cikin kasa” ya na mai shan alwashin cewa zai kawo karshen abin da ya kira, “bore da karan-tsaye ga doka a fadin kasar.”
Trump ya ce zai yi amfani da dukkannin kayan aiki da gwamnatin tarayya ke da su, da na soji da na farar hula, wajen tsayar da boren da kuma wasoson da ake ta yi.
Jim kadan da fara jawabin Shugaban kasar, manema labarai da ke jira a wurin shakatawar nan na Rose Garden sun yi ta jin fashe-fashe masu karfi na barkwanon tsohuwa a wajejen wurin shakatawar nan na Lafayette Park, inda ‘yan sanda suka ja daga da masu zanga-zanga.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 23, 2021
Jirgin Hukumar Sama Jannatin Amurka Ya Isa Tashar Sararin Sama
-
Fabrairu 22, 2021
COVID-19 :Adadin Wadanda Suka Mutu Ya Kusa Rabin Miliyan A Amurka
-
Fabrairu 20, 2021
Amurka Ta sake Komawa Cikin Yarjejeniyar Sauyin Yanayi A Hukumance
-
Fabrairu 17, 2021
Texas-Dussar Kankara Ta Haifar Da Dauke Wuta A Gabashin Amurka
-
Fabrairu 14, 2021
Yadda Majalisar Dattawan Amurka Ta Wanke Trump
Facebook Forum