Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ta Leko Ta Koma: Rigakafin COVID-19 Daga Rasha


Yekuwar samar da rigakafin cutar Coronavirus daga kasar Rasha dai ta leko ta koma a cewar jami'an kiwon lafiyar Najeriya.

Ma'aikatar Kiwon Lafiyar kasar ta fito karara inda ta yi bayani cewa gwamnatin kasar Russia ta bada gudumawar rigakafin cutar Coronavirus wanda Ministan Ma'aikatar Kiwon lafiyan Najeriya, Farfesa Osagie Ehanire ya fito fili ya bayyana.

Sai kuma kwatsam jami'in watsa labarai na Ma'aikatar Olujimi Oyetomi ya fitar da sanarwa da ke nuna subul da baka ne suka yi ba rigakafin Coronavirus ba ne ya samu, amma wai wani sarari ne kasar Russia ta ba Najeriya ta yi bincike akan rigakafin.

Wannan romon baka da Ministan Kiwon Lafiya Farfesa Osagie Ehanire yayi wa al'umman Najeriya ya jawo suka da zargi da kuma zato kan wanan salo da Mahukuntan suka dauka da ya shafi wanan rigakafin.

Babban Jami'i a Ma'aikatar Kiwon lafiya, Dokta Ibrahim Kana, ya yi bayani cewa Jakadan Kasar Russia ne ya kawo ziyara ga Ministan Kiwon lafiya kuma a lokacin da suke bayani ne ya ba Minista wani sarari na sanin abinda rigakafin ya kunsa amma har yanzu Najeriya ba ta karba ba kuma.

Cutar Coronavirus dai ta yi sanadiyar rasuwar likitoci 14 a yayinda kuma bayani ya nuna wasu 321 sun kamu da wanan cutar inda 68 suka samu warkewa, duka duka dai jami'an kiwon lafiya 812 ne suka kamu da wannan cutar ya zuwa yanzu

Saurari rahoton Madina Dauda cikin sauti

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00


Facebook Forum

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG