Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ta Yiwu a Haramta Achaba a Najeriya


Majalisar Sufuri a Najeriya tayi babban taronta na shekara shekara a karshen wannan mako a Jihar Enugu dake kudancin Najeriya.

A karshen wannan taro da aka gudanar ranar Asabar, majalisar ta yanke shawarar cewa akwai yiwurar haramta sana’ar acaba, ko kuma kabu kabu a duk fadin Najeriya, da nufin samar da wani sabon tsarin sufurin jama’a mai inganci.

Ministan Sufuri a Najeriya Sanata Idris Umar ya amince da wannan mataki.

Alhaji Babangida Shehu Mai Hula, shine shugaban Hadaddiyar Kungiyar ‘Yan Achaba a Najeriya.
“Na dauki wannan labari, kamar kowane labari da gwamnati take da shi na bukatar cigaba”.

Wannan sana’ace dai da mutane keyi saboda neman abin da zasu ciyar da iyalinsu, idan kuma har gwamnati zata hana wanna sana’a to saita taimaka samarwa masu wata sana’a. ga hirar Halima Djimrao da Alhaji Babangida Shehu Mai Hula, shine shugaban Hadaddiyar Kungiyar ‘Yan Achaba a Najeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:09 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG