Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taba Na Illa Ga Daukacin Jikin Dan Adam – Likita


Shan Taba Sigari a Afrika.

Yau Lahadi 31 ga watan Mayu, rana ce da hukumar lafiya ta duniya, WHO ta ware domin ci gaba da fadakarwa kan illar da tabar sigari ke yi ga dan adam.

Kamar sauran kasashen duniya, jami’an kiwon lafiya a matakai daban daban, na yin amfani da wannan ranar suna fadakarwa kan irin illar da tabar sigari kan haifarwa jikin dan adam.

“Wannan rana ta na da muhimmanci ba ga likitoci ba, har ma ga jama’a baki daya, saboda rana ce da aka ware domin a takaita yadda ake shan taba, sannan ranar ta na ba da damar a duba a ga me ya kamata a yi nan gaba.” Inji Dr Usman Muhammad, kwararren likita kuma darekta a matakin farko na ma’aikatar lafiyar jahar Naija.

A cewarsa matsalar tabar sigari ita ce tana illa ga daukacin jikin dan adam, sannan wandanda ke kusa da mai sha suma suna cutuwa daga hayakin da suke sheka.

“Wadanda suke shan taba, su daina, tun da ba wani abu ne mai amfani .” Dr. Muhammad ya kara da cewa da aka tambaye shi mai ya kamata masu sha su yi.

Malam Ahmad Abdullahi Tela, wani mutum ne da ya daina shan tabar sigari baayn da ya kwashe shekaru biyar yana zuka, ya kuma cec irin banbancin da ya ke ji a jikinsa yanzu ya fi na da.

“Na kai shekara biyar ina shan taba lokacin ina saurayi daga nan kuma na ga abin akwai cutarwa, domin ko wani aiki na yi na karfi sai na dinga haki. Amma yanzu da na daina lafiya a jiki na koda ba a ce sigari haram ba ce akwai banbanci.” Inji Abudallahi Tela.

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG