Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tabarbarewar Ilimi a Najeriya


Irin wuraren da yara ke zuwa makaranta
Irin wuraren da yara ke zuwa makaranta

Sakamakon jarabawar sakandare ta bana ta sake jaddada tabarbarewar ilimi a Najeriya fiye da yadda ake tsammani

An dora tabarbarewar ilimi kan abubuwa da dama.

Dalilan tabarbarewar ilimin a Najeriya sun hada da hukumomi da malamai da iyaye da daliban.

Rashin isassun kwararrun malamai na cikin dalilai na musamman da suka haddasa tabarbarewar ilimi a kasar. Sakamakon jarabawar bana ya nuna cewa kashi 62 na daliban da suka yi jarabawar basu sami maki na a zo a gani ba musamman a darusan lissafi da turanci.

Malam Abdullahi Yalwa na kwalajin kere-kere yace ilimi ya koma baya saboda naurorin hannu na yanzu da suka dauke hankalin dalibai. Na biyu babu alaka tsakanin hukumar dake shirya jarabawar da ma'akatar ilimin Najeriya. Abun da za'a koyas da yara daban tambayoyin da zasu fito kuma daban ne.

Malam Yusuf Muhammad jami'in yaki da jahilci yace babu cikakkun litattafai na koyon daratsi. Ana yawan sake littafai da sukan kawo rudani.

Akwai matsalar rashin daukan malaman da suka dace. Duk wanda zai koyas yakamata a ce yana da ilimin koyaswa din . Saboda rashin aikin yi kowa ya samu digiri sai ya nemi aikin koyaswa.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:08 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG