Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tabin Kwakwalwa: An Ja Hankulan Mahukunta


Wani ma'aikacin kiwon lafiya ya na wanke hannuwansa bayan kula da mara lafiya

Masana a fannin kula da lafiyar kwakwalwa, sun yi kira ga hukumomi da su maida hankali wajen kulawa da fannin masu fama da wannan matsalar, domin ya na bukatar kulawarsu.

A cewar Dr Musa Gambo, kwararre a fannin kula da masu tabin hankali, a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, ya ce wannan larura ce da ke daidai da sauran larurori da ke jikin mutum.

“Jama’a a gane, wadannan larurori ne da su ke kamar sauran na bangarorin jikin mutum, suna jin magani kuma wadanda su ke da larurar tabin kwakwalwa ba za su iya yadawa mutum ba saboda ya na zama da su ko kuma kulaa da su ba.” In ji Dr. Gambo.

Ya kara da cewa “ya kamata a cewa kowane asibiti a ce an bude sashen na masu kula da wannan bangare, ba sai an ware asibiti, an ce wannan shi ne na masu kula da larurar kwakwalwa ba, hakan na sa mutane ba sa san zuwa wurin saboda an riga an shafa mai jan penti.”

Dr. Gambo ya kara da cewa ya kamata hukumomi su gane cewa, wani abu da ya fi muhimmanci a jikin dan adam shi ne hankali.

“Za a iya kula da wannan banagren, wajen samar da kayyaki, wajen ba da kwarin gwiwa da yin bincike a wannan bangare.” Ya ce.

Wadannan kalamai na Dr Gambo, na zuwa ne kwanaki biyu bayan da aka yi bikin tunawa kan yadda za a rinka tallafawa masu fama da wannan matsala, musamman ta hanyar mutunta su.

Ko yaya iyaye da ‘yan uwan wadanda ke fama da larurar tabin hankali ke kayawa a rayuwarsu ta yau da kullum, domin jin karin bayani, saurari wannan rahoto na Mahmud Ibrahim Kwari, wakilin Muryar Amurka a Kano.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG