Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tafiyar Buhari Kasar Waje Barnar Kudin Kasa Ne - Dr. Yazid


Shugaba Muhammadu Buhari.
Shugaba Muhammadu Buhari.

Masu sharhi sun fara kushe tafiyar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai yi zuwa Ingila domin duba lafiyarsa, matakin da suka bayyana a matsayin barnar kudin kasa.

Tun bayan sanarwar da mai baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari, shawara a harkokin watsa labarai Femi Adeshina ya fitar a jiya Litinin, wadda ke bayyana cewar shugaban zai yi balaguro zuwa kasar Burtaniya, don duba lafiyarsa kamar yadda ya saba, 'yan Najeriya suka shiga caccakar fadar da yin Allah wadai.

A ranar Talata ake sa ran shugaban na Nijeriya Muhammadu Buhari, zai kama hanya zuwa Ingila domin duba lafiyarsa da yake yi shekara-shekara.

Sanarwar ta kara da cewar shugaban zai dawo a tsakiyar watan Afrilu, amma kamun ya kama hanya zai yi wata ganawa ta musamman da hafsoshin tsaron kasar.

Karin bayani akan: Dr. Abu Yazid, Korona, Burtaniya, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

A hirarsa da manema labarai, mai magana da yawun shugaban Garba Shehu, ya bayyana cewa "Ai wannan tafiyar ba bakon abu ba ne, dama sama da shekaru 30, yakan yi irin wannan ziyara ta ganin likitocin shi, amma Annobar Korona ce ta hana shi tafiya har na fiye da tsawon shekara daya."

Don haka yanzu zai tafi, don ganin ya bi umurnin likotocinsa, kuma gwamnati na iya bakin kokarinta na ganin ta inganta asibitocin kasar da kayan da suka dace.

Garba Shehu, ya kara da cewa, saboda irin yunkurin gwamnatin ta su, hukumar lafiya ta duniya ta yaba musu a makon da ya gabata, na irin namijin kokarin da suke yi a yaki da annobar Korona.

Masu fashin baki na kallon wannan tafiyar tasa a matsayin gazawa wajen samar da kayan aiki nagartattu don tallafawa fannin kiwon lafiyar kasar, wanda yanzu haka kungiyar likitocin kasar ta bayyana shirinta na shiga yajin aiki a ranar Alhamis, idan har ba a biya mata bukatunta ba.

Dr. Abu Yazid, kwararren likita ne a Najeriya, wanda ya danganta irin wannan dabi'ar ta shugabannin a Najeriya fita kasashen ketare don samun jinya, yana ganin dalilin ba komai ba ne illa "rashin samar da kayan aiki na gari, hakan ya sa ba su da natsuwa da likitoci da kayan aiki a kasar."

Ya kara da cewar "babu irin likitoci da kasashen waje ke da su da babu irin su a Najeriya, don haka barnatar da dukiyar kasa ne kawai ke kai su ga irin wadanna tafiye-tafiyen marasa tushe."

Saurari rahoton Umar Farouk Musa cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG