Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Yi Damarar Hana Shiga Da Riga-kafin COVID Na Jabu


Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari

Gwamnatin Najeriya ta yi matashiya ga hukumomin kasar game da labarin da ake yadawa kan allurar rigakafin COVID-19 na jabu da ake ce za a shigo da su a Afrika.

Hukumomin sun kuma kawar da fargabar cewa ana bada rigakafi mai cutarwa ko kuma wasu hukumomi da basu da izini suna sayar da allurar rigakafin.

Adebimpe Adebiyi, darektan hukumar kula da ayyukan asibitoci, a ma’aikatar kiwon lafiya ta tarayya, ya fitar da wata sanarwa a kan wannan batu.

Sanarwar ta biyo bayan wata wasikar da kwamitin shugaban kasa mai yaki da COVID-19 ya fitar game da gano dubban allurar riga-kafi ta jabu da za a shigo da ita Afirka daga China.

Adebiyi ya ce kafin a iya hana shigowa da riga-kafin jabun, ya kamata ma’aikatar Kwastam ta Najeriya ta kebe filin sauka da tashin jiragen sama na kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe a Abuja a matsayin hanya daya tilo da za a rika shiga da allurar rigakafin a Najeriya.

Gwamnati ta ja hankalin darektocin kiwon lafiya a asibitocin tarayya da sauran hukumomin kiwon a kan wannan batun.

Najeriya ta samu zubin riga-kafin miliyan 3.94 na rigakafin Oxford-AstraZeneca, a karkashin shirin tallafin riga-kafi na kasa da kasa na COVAX a farkon watan Maris.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG