Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Indiya ta Cika Shekaru Uku ba Tare da Bullar Polio ba


Wata ma'aikaciyar lafiya a Indiya tana ba yaro maganin rigakafin Polio a New Delhi, 7 Afrilu 2013
Wata ma'aikaciyar lafiya a Indiya tana ba yaro maganin rigakafin Polio a New Delhi, 7 Afrilu 2013

Hukumar Kiwon lafiya ta Duniya tana shirin ayyana kasar Indiya a zaman wadda ta samu nasarar kawar da cutar Polio, ta fita daga jerin Najeriya, Pakistan da Afghanistan.

A ranar litinin ne kasar Indiya ta cimma wata tazarar da aka yi zaton cewa zai yi wuya ta cimma: watau ta cika shekaru uku cur ba tare da samun rahoton bullar cutar Polio ko sau day aba, abinda ya share fagen ayyana kasar a zaman wadda ta samu nasarar kawar da Polio.

A ranar 13 ga watan Janairun 2011 aka samu rahoton bullar Polio ta karshe a Indiya, a jikin wata yarinya mai shekara biyu da haihuwa a Jihar Bengal ta Yamma.

Shekaru uku ba tare da samun bullar wannan cut aba, na nufin cewa a yanzu, Hukumar Kiwon lafiya ta Duniya zata ayyana kasar a zaman wadda ta samu nasarar kawar da Polio.

A yanzu, Najeriya da Pakistan da kuma Afghanistan, sune kadai kasashen duniya da suka rage da cutar Polio.

Kafin shekarun 1950, cutar Polio ko shan Inna, tana gurguntar da dubban mutane a kasashe masu arziki na duniya. Kwayar cutar tana kama jijiyoyin aikewa da sakonni na jikin mutanen, kuma cikin ‘yan sa’o’I kalilan da kama mutum, tana iya haddasa gurguntar da ba za a iya maganinta ba.

Cutar mai saurin yaduwa, ta fi bazuwa a wurare marasa tsabta, abinda ya sa ta jima tana addabar kasar Indiya. Sai dai kuma, Polio cut ace da za a iya shawo kanta a ja mata burki, amma sai ta hanyar bayar da maganin rigakafi ga daukacin al’ummar wurin da take. Cutar ta fi kama yara ‘yan kasa da shekara biyar.

A shekarar 2009, mutane 741 suka kamu da Polio a kasar Indiya, watau kusan rabin dukkan wadanda suka kamu da Polio a fadin duniya a wancan shekarar. A shekarar 2010, mutane 42 kacal suka kamu, kuma a shekarar 2011, mutum daya tak, wata karamar yarinya ta kamu da wannan cuta. Wannan it ace ta jkarshe a kasar.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG