Accessibility links

Takaddama ta Kunno Kai Tsakanin Majalisar Dokoki da Gwamnatin Jihar Neja


Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja
A jihar Neja wata takaddama ta taso tsakanin majalisar dokokin jihar da gwamnati.

Majalisar dokokin jihar Neja ta nuna rashin gamsuwa da ayyukan cigaba da gwamnatin jihar tace ta yi a kananan hukumomi ashirin da buyar dake jihar. Kwamitin dake kula da harkokin kananan hukumomi na majalisar shi ne ya gudanar da wani rangadin gani da ido a duk kananan hukumomin inda ya gano abun takaici na rashin samun abun da ya kamata a yankunan kananan hukumomin.

Nurudeen Umar daya daga cikin 'yan kwamitin din yace sun zagaya duk kananan hukumomin guda ashirin da biyar sun kuma gano gwamnatin jiha bata basu kudi ba. Yace kowa ya san ba abun da za'a iya yi idan babu kudi. Ayyukan da suka yi sun yi ne bisa ga abun da aka basu kuma abun da aka basu bai taka kara ya karya ba. Zagayen ya nuna cewa akwai nukunuku a shirin da gwamnatin jihar ta fito da shi da nufin raya karkarar jihar kamar shirin samarda hanyoyi masu tsawon kilomita goma goma a kowace karamar hukuma.

Majalisar ta gano cewa a cikin kananan hukumomi ashirin da biyar, a cikin uku kacal aka kammala aikin hanyoyi tun lokacin da aka fara shirin a shekarar 2010. A wani gefen kuma majalisar tace akwai lauje cikin nadi a shirin raya mazabu 274 a fadin jihar. A karkashin shirin ana baiwa kowace mazaba nera miliyan kowane karshen wata lamarin da majalisa tace ta gano akwai tsallake.

Dangane da matakin da majalisar zata dauka dan majalisa Nurudeen Umar yace zasu rubuta rahotonsu su mikawa majalisa inda za'a karanta kuma gwamna zai sami kwafi na rahoton. Shugaban kwamitin raya mazabu a majalisar Abdullahi Lawal yace doka ce ta basu damar gudanarda zagayen domin duba abun da aka yiwa talakawa. Yace su ne suka yi dokar kashe kudi domin haka dole ne su tabbatar da yadda aka kashe kudin da suka kayyade.

Gwamnatin jihar ta mayarda martani kan lamarin. Alhaji Yusuf Tagwai kwamishanan kananan hukumomi da masarautu yace talaucin da jihar ta fada ciki shi yayi sanadiyar rashin kammala ayyuka a wasu kananan hukumomin. Yace idan 'yan kwangila sun yi aiki ba zasu cigaba ba sai an biyasu. Karancin kudi shi ne ya kawo cikas.

Ga rahoto.

XS
SM
MD
LG