Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaddamar Bincikar Atiku a Abuja


Tsohon Mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban Najeriyar, wanda zai yi takarar shugabancin kasar karkashin Jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya yi korafin cewa an ci zarafinsa saboda irin binciken da aka masa a filin tashin jirage na Abuja.

Yayin da zaben 2019 ke ci gaba da karatowa, al’amuran da masu fashin baki ke ganin sun shafa ko kuma ake ganin suna da nasaba da zaben na ta bayyana ta fuskoki da dama.

Wani batu na baya-bayan nan da ya auku, wanda ya ja hankulan ‘yan kasar da dama shi ne batun bincikar tsohon mataimakin shugaban kasar, Atiku Abubakar da aka yi a filin tashin jirage na Nnamdi Azikwe a Abuja a jiya Lahadi.

Jami’an shige-da fice ne suka binciki Atiku, dan takarar da zai fafata da shugaba Muhammadu Buhari a zaben na badi.

Atiku ya dawo ne daga birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, inda ya sauka a birnin na Abuja.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriyar, wanda zai yi takarar shugabancin kasar karkashin Jam’iyyar adawa ta PDP, ya yi korafin cewa an ci zarafinsa saboda irin binciken da aka masa.

“Na iso birnin Abuja da safiyar yau (Lahadi) inda jami’ai suka bincike ni da zimmar saka ni da ma’aikata na cikin fargaba.” Atiku ya rubuta a shafinsa na Twitter.

Tuni wannan labari ya karade kafafen sada zumunta inda masu suka da yabo suka yi ta muhawara akai.

Amma fadar gwamnatin Najeriya ta yi wuf ta mayar da martani, tana mai musanta cewa binciken an yi shi ne da wata manufa.

Sai dai ba ta musanta aukuwar lamarin ba.

“A duk lokacin da wani jirgi mallakar mutum ko na shata ya iso, kamar yadda dan takarar jam’iyar PDP ya shigo, jami’an shige da fice da na tsaro kan tare su,” su gudanar da bincike akansu. Inji Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika.

Ya kuma kara da cewa, “an girmama tsohon mataimakin shugaban kasar” daidai yadda mukaminsa yake a Najeriya.

“Dole ne a yi irin wannan bincike, kuma an saba yinsu a ko ina a Duniya” Sirika ya kara da cewa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG