Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takunkumi: Turkiyya Ta Mai Da Martani Ma Amurka


Turkish President Tayyip Erdogan makes a speech at the Presidential Palace in Ankara, July 15, 2018.
Turkish President Tayyip Erdogan makes a speech at the Presidential Palace in Ankara, July 15, 2018.

Rigimar Amurka da kasar Turkiyya dai na dada kazancewa ta yadda kasar Turkiyya ta mai da martani kan Amurka wacce ta kakaba ma ta takunkumi saboda cigaba da dauri wani pastor ba-Amurke kan zargin ta'addanci.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, jiya Asabar ya ba da sanarwar daukar matakan ramuwar gayya kan Amurka, sanadiyyar kakaba takunkumin da Amurka ta yi ma wasu Ministocin Turkiyya biyu saboda cigaba da daure wani Pastor ba-Amurke.

Erdogan ya bayyana wadannan matakan ne yayin da yak e jawabi a wani taron jam’iyyar mata a birnin Ankara. Ya ce, “Mun kai zuciya nesa har zuwa yammacin jiya. Yau ina bayar da umurnin kama kaddarorin Sakataren Harkokin Shari’ar Amurka da kuma Sakataren Cikin Gida a kasar Turkiyya,” a cewar Erdogan.

Erdogan ya kara da cewa, “Masu ganin kamar za su iya sa Turkiyya ta tsorata ta wajen furta kalaman barazana da kuma kakaba takunkumi marasa kan gado lallai ba su san kasar Turkiyya ba.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG