Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takunkumi Ya Haifar Da Koma Bayan Tattalin Arzikin Sudan-al-Bashir


Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir
Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir

Shugaban Kasar Sudan Omar al-Bashir ya yi jawabi ga magoya bayansa a Khartoum, yayinda aka shiga wata sabuwar zanga zanga a babban birnin kasar.

Shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir ya fadawa taron magoya bayansa jiya talata cewa wannan kokarin nasu na futowa da suka yi domin su saurare shi ya aika sako karara ga wadanda ya kira "masu cin amanar kasa, da lalata kayan gwamnati da kuma sojojin haya" dake zanga zangar kin jinin gwamnatinsa.

Wani hoton bidiyo da ake ta yadawa a kafofin sada zumunta ya nuna dandazon mutane suna zanga zanga a Khartoum, babban birnin kasar Sudan ranar Talata, na nuna adawa da matsin tattalin arziki da suke fuskant, yayinda suke kira ga shugaban da ya sauka daka mukamin sa.

Wani gangamin jam’iyyun siyasar kasar da kungiyar kwadago sun bukaci magoya bayan su, da su fito su bukaci Bashir ya sauka daka kujerar shugabanci kasar.

A daidai wannan lokacin ne kuma, shugaba Bashir yake yiwa taron magoya bayansa bayani a garin Wad al Madina na jahar Jezira, inda ya gaya musu cewa wannan matsin tattatlin arzikin da suka shiga ya samo asali ne daga takunkumin da kasashen waje suka kakabawa kasar.

Amurka ta janye takunkimin tattalin arziki a watan Oktoba, amma duk da haka darajar kudin kasar yayi mummunar faduwa.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG