Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Talauci Bai Hana 'Yan Niger Zuwa Aiki Kan Lokaci Ba


Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar

Duk da talauci da rashin bunkasar tattalin arziki da kasar Niger ke fama dasu a jerin kasashen duniya amma 'yan kasar suna zuwa aiki akan lokaci sabanin yadda lamarin yake a wasu kasashe da suka fita wadata.

Hakan kuwa ya faru ne ta hanayar wani tsari da shugaban kasar Niger din ya fito dashi na sake mayar da 'yan kasar a guraben aiki. Hakan ya zama tamkar misali ga wasu kasashen duniya musamman irin su Najeriya mai arzikin man fetur.

Wakilin Muryar Amurka da ya zagaya babban birnin kasar Niamey ya ga motoci suna ta tafiya ba gaggautawa domin kada su makara zuwa aiki. Karfe takwas na safe suke shiga aiki amma da wuya ma'akata su makara. Hakan nada nasaba ne da sauya dabi'o'in 'yan kasan ne. Shugaban kasar Yusuf Muhammadu ke kan gaba domin sauya tarbiyar 'yan kasar na rashin girmama aikin gwamnati da kuma dukiyar kasa da su keyi da.

A ranar da aka rantsar da shugaban kasar yace yayi rantsuwa da Kur'ani mai tsarki domin rantsuwar yace yana bukatar duk wadanda zasu rike iko tare da tallafin 'yan Niger na sauya dabi'o'i wajen aiki da aka yi watsi dashi. Shugaban yace yakamata suyi watsi da mugayaen dabi'o'insu su kuma sauya dabi'o'insu na yau da kullum. Tun daga lokacin shugaban ya fara girmama ayyukan gwamnati inda shi da kansa ya kan kai ziyarar bazata a wasu ofisoshin gwamnati a lokacin shiga aiki.

Ana fara aiki karfe takwas na safe. Lokaci na yi kuwa za'a ga mutane tsaf a wurin aiki domin idan mutum ya makara za'a dauki mataki. Malam Hassan Sani babban jami'i ne a ma'aikatar ministan kwadagon kasar yace suna da wata doka dake kula da duk wani ma'aikacin kasar. Ma'aikaci da yayi laifi sai a tuhumeshi a karkashin dokar.

Daukan matakan ladaftar da masu laifi na cikin ababen da suka kara maido da martabar ma'aikatun gwamnati. Amma Malam Iro Bubakar yana ganin kamata yayi gwamnati ta tsarawa kowa aikin da zai yi kowace rana ta kuma gwadashi akan abun da ta bashi yayi. A daina barin mutane suna zuwa aiki cikin duhu.

Maida ma'aikata suyi aiki daidai ne domin da mutane basa aikin komi a gwamnati inji wasu ma'aikata. Wannan kuma yakamata ya faro daga sama domin na kasa ya gani yayi koyi dashi. Shugabanni su bada misali, su yi aiki yadda yakamata.

Harsashe ya nuna cewa gwamnati zata kashe kudin kasar kimanin miliyan dubu uku da 'yan kai akan karin albashi da alawus kowace shekara domin ba ma'aikata sukunin yin aiki a cikin yanayi mai kyau. To saidai wasu ma'aikatan suna kukan rashin kayan aiki.

Ga rahoton Abdullahi Mamman Ahmadu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:20 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG