Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taliban Ta Ce Ta Fara Tattaunawa Da Amurka a Afganistan


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

A wani al'amari mai ban mamaki, kwatsam kungiyar Taliban mai tsattsauran ra'ayi ta ce ta fara ganawa da Amurka kan yadda za a kawo karshen yakin da aka dade ana yi a Afganistan.

Kungiyar Taliban shiyyar Afghanistan ta tabbatar cewa ta shiga tattaunawar kai tsaye da Amurka a kasar Qatar a wannan mako mai shudewa, kan yadda za a daidaita saboda a kawo karshen yakin da aka shafe shekaru 17 ana yi a kasar ta Afghanistan.

Wani babban jami'in kungiyar Taliban ya gaya wa Muryar Amurka jiya Jumma'a cewa, Mataimakin Mukaddashin Sakatare Mai Kula da Kudanci da kuma Yankin Tsakiyar Asiya, shi ne ya jagoranci tawagar ta Amurka a ganawar ta Doha.

Da ya ke magana bisa sharadin sakaya sunansa, wani babban jami'in kungiyar Taliban ya yi bayanin cewa taron na sharar fage, ya mai da hankali ne kan yadda za a yi shinfida mai kyau don tuntuba da kuma ganawa ta gaba tsakanin Amurka da Taliban din.

To amma Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ki cewa komai kan wannan rahoto na ganawa tsakanin Amurka da mayakan Taliban.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG