Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taliban Ta Kai Wani Hari A Afghanistan


Wasu mayakan Taliban

Hukumomi a Afghanistan, sun ce wasu hare haren da kungilar Taliban ta kai a arewacin kasar, sun yi sanadin mutuwar jami’an tsaro akalla 17 baya da wasu da dama da su ka jikkata.

Wannan tashin hankalin na zuwa ne a daidai lokacin da bangarorin da ke fada a Afghanistan, ke shirin ganawa a kasar Qatar a wannan watan, don share fagen wani zagaye na tattaunawar zaman lafiya.

Wani mai magana da yawun gwamnati a lardin Jawzjan na arewacin kasar, ya gaya ma Muryar Amurka cewa, ‘yan tawaye sun abka ma wasu wurare biyu da aka girke sojoji don tsaro a lardin Aqcha, inda su ka zo cikin dare daga bangarori daban daban, a wani yinkuri na kama sojojin.

Marouf Azar ya ce an yi ta fafatawa har zuwa asuba, aka kashe sojojin Taliban 12 aka kuma raunata biyar. Su ‘yan Taliban din kuma sun yi awon gaba da sojojin gwamnati hudu a cewarsa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG