Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taliban Ta Kwace Ikon Afghanistan, Ashraf Ghani Da Mataimakinsa Sun Bar Kasar


Taliban fighters sit over a vehicle on a street in Laghman province on August 15, 2021.

Shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani tare da mataimakinsa da kuma wasu manyan jami’an gwamnatin sa, sun bar kasar yau Lahadi, lamarin da ya bai wa mayakan Taliban dama su sake komawa kan mulki bayan shekara 20 da sojojin da Amurka ke wa jagoranci suka hambarar da su daga kan karagar mulki.

Manyan mambobin sojin Taliban sun isa fadar shugaban kasar a Kabul yayin da mayakan Taliban suka karbe iko da wurare masu muhimmanci a babban birnin kasar.

A yau Lahadi da yamma Kakakin kungiyar Taliban, Zabihullah Mujahid, ya tabbatar da cewa an umarci mayakan da su tsare ofisoshin tsaro da cibiyoyi a Kabul don hana tashin rudani da sata bayan sojojin Afghanistan sun yi watsi da su.

Mujahid ya bukacin mazauna birnin da su kwantar da hankalinsu, yana cewa wannan matakin an dauke shi ne don tabbatar da tsaron lafiyar jama’a.

Sai dai har yanzu babu wani jawabi daga Ghani tun bayan da ya fice daga Kabul. A wani sako da aka nada a ranar Asabar, ya fada wa kasar cewa wasu yan kasar da kasashen duniya da suke taka rawa kan lamari sun tuntube shi lamarin da ya kira da kaddamar da yaki.

Shugaban kwamitin Sulhu na Afghanistan, Abdallah Abdallah, ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na facebook, yana caccakar Ghani.

Abdallah ya tabbatar da cewa Ghani ya fice daga Afghanistan kuma ya ce, Inajin tsohon shugaban kasar ya fice daga kasar kuma ya bar mutane a cikin mummunan hali. Allah kuma zai masa hisabi.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG